13 Faburairu 2020 - 08:14
Iraqi: An Dawo Da Zaman Lafiya A Birnin Bagdaza

A wannan makon da muke ciki ne aka kawo karshen zanga-zanga a manya-manyan titunan birnin Bagdaza da kuma wasu biranen kasar Iraqi.

(ABNA24.com) A wannan makon da muke ciki ne aka kawo karshen zanga-zanga a manya-manyan titunan birnin Bagdaza da kuma wasu biranen kasar Iraqi.

Labaran da suke fitowa daga birnin Bagdaza babban birnin kasar sun nuna cewa jami’an tsaro sun bude manya-manyan tituna wadanda aka rufe su na tsawon watanni da suka gabata.

Hukumomin da suke kula da lamuran zamantakewa a cikin birnin sun bada sanarwan cewa an bude makaranto da ofisoshin gwamnati a ranar laraba wato jiya. Sannan harkokin kasuwanci sun kuma kamar yadda suke.

Har’ila yau ma’aikatan tsabataci birnin sun fara shashare manya-manyan tituna da shatele-teleloli da kuma manya-manyan wurare a cikin birnin.

A halin yanzu dai gwamnati ta takaida zanga-zanga a dandalin Tahril da ke tsakiyar birnin Bagdaza, sannan ta ce dukkan masu zanga-zanga zasu sami kariyar jami’an tsaro a duk lokacinda zasu gudanar da ita.



/129